Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Alhamis

13 Afirilu 2023

08:41:27
1357804

Iran: Sahayoniyawan suna gaggawar gushewarsu, amma za mu yi aikin da ya hau kanmu a ranar Kudus

Shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi ya bayyana cewa: Sahayoniyawan suna fada a tsakanin su, kuma suna gaggawar halaka kansu, amma za mu gudanar da ayyukanmu na siyasa da addini a ranar Qudus.

Kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Baiti (A.S) ABNA ya ruwaito - Sayyid Ibrahim Raisi, a cikin tarukan raya daren ashirin da daya ga watan Ramadan da kuma Lailatul Kadri a haramin Imam Khumaini. (Allah Ya yarda da shi), ya jaddada muhimmancin jihadin tawili a cikin al'umma, yana mai cewa: "A yau ya kasamce muna ganini kyamar Iran da kyamar Musulunci tana yaduwa a duniya, don haka wajibi ne mu zauna mu tattauna da matasa, mu yi magana, mu bude hadaddun tunani na matasa, dukkan jami'ai, malaman jami'a, malamai, masu wa'azi, da dalibai su sani cewa makomar kasa tana hannun matasa.


Shugaban kasar ya yi ishara da umarnin Imam Ali (AS) inda ya kara da cewa: “Batu na asali a cikin umarnin Amirul Muminin (a.s) shi ne kada a so duniya, kuma abu na gaba shi ne tsayawa tsayin daka gaba ga azzalumi da kare wanda aka zalunta….Muna tsaye tsawon shekaru arba’in da ’yan kadan a bangaren mutanen da ake zalunta a Palastinu, kuma a ranar Kudus duk shekara muna shaida irin yadda musulmi suke shiga cikin jerin gwano, a bana ma ta hanyar mu Shiga Tattakin Kudus, za mu nuna cewa mun tsaya tare da wanda aka zalunta a kan azzalumi.


Ya yi ishara da manyan bambance-bambancen da ake samu a Isra'ila yana mai bayanin cewa: Sahayoniyawan suna fada a tsakaninsu kuma suna gaggawar halaka kansu, amma da yardar Allah za mu cika aikinmu na siyasa da addini a ranar Qudus.


Shugaban ya bayyana cewa, dukkanmu muna da wani nauyi da ya rataya a wuyanmu a kan wadanda suke kewaye da mu, sannan ya ce: "Dole ne mu mai da hankali kan kur'ani, bisa albarkar juyin juya halin Musulunci mun samu sha'awar kulawa da kur'ani a cikin kasarmu, amma hakan ya zama wajibi a gare mu amma dole ne a kara wannan bada muhimmanci".