Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

12 Afirilu 2023

07:50:43
1357667

Sheikh Isa Qassim: Gaba Dayan Al'ummar musulmi Ke Da Alhakin Dakile Hare-haren Yahudawan Sahyoniya A Kan Al-Aqsa

Sheikh Qassim ya tabbatar da cewa, bisa sharia dukkanin al'ummar musulmi ne ke da alhakin dakile mamayar haramtacciyar kasar Isra'ila tare da hana yahudawan sahyoniya su ci gaba da kai farmaki kan masallacin Al-Aqsa.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti (a.s) - ABNA - ya kawo rahoton cewa: Ayatullah Sheikh Isa Qassim ya tabbatar da cewa: al'ummar musulmi ne ke da alhakin mayar da martani kan harin da yahudawan sahyuniya suka kai a kan masallacin Al-Aqsa.


Sheikh Qassim ya tabbatar da hakan a shafinTwitter a shafinsa na Tuwita cewa "dukkan al'ummar musulmi a bisa sharia ne ke da alhakin dakile mamayar Isra'ila tare da kin barin yahudawan sahyoniya su ci gaba da kai farmaki kan masallacin Al-Aqsa."

Kuma ya yi gargadin cewa "ketara iyaka da yahudawan sahyuniya suke yi wa Al-Aqsa da musulmin da suke zaune a cikinsa suke Iitikafi, tamkar tauye martabar masallacin ne, da keta alfarmar Musulunci da yaki da bautar Allah."