Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

25 Maris 2023

13:36:29
1354089

Siriya: An Kaiwa Wasu Sansanoni Biyu Na Mamayar Amurka Mummunan Hari

An Kaiwa Wasu Sansanoni Biyu Na Mamayar Amurka A Deir Ezzor Dake Gabashin Syria Hari Da Makami Mai Linzami Sama Da 20.

An ba da rahoton cewa, wasu makamai masu linzami sun fada kan sansanin sojojin Amurka da ke cikin filin iskar gas na "Koniko", ba tare da samun bayanai kan yawan asarar da aka yi ba.


Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahlul Biyt As ABNA ya habarto cewa, an kai hare-hare da makami masu linzami kan sansanonin sojojin Amurka Mamaya biyu da suka hada da "Al-Omar" da kuma "Koniko" a yankin Deir Ezzor dake gabashin kasar Siriya.

An ba da rahoton cewa, makamai masu linzami da dama sun fada kan sansanin sojojin mamaya na Amurka da ke cikin filin iskar gas na "Koniko", ba tare da bayanin girman asarar da aka yi ba, yayin da tashar Al-Alam ta ruwaito cewa, sama da makamai masu linzami 20 ne suka afkawa sansanin da aka ambata a baya.

A halin da ake ciki, tashar Al-Alam ta nakalto majiyar Syria na cewa gobarar ta tashi ne a sansanin "Vanguard" da ke Deir Ezzor da kuma sansanin "Koneko", bayan an kai musu wasu hare-hare.

Majiyar ta sanar da wani zazzafar tashin jirage masu saukar ungulu na Amurka a kan filin "Koniko", da ke gabashin kogin Fırat.

Wani yanayi na firgici da Tashin hankali ya tashi a tsakanin fararen hula a kauyuka da garuruwan da ke kusa da sansanin Amurka a filin "Koniko" da ke arewacin Deir ez-Zor.