Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Laraba

15 Maris 2023

18:57:15
1352389

Gudunmawar da Shahid Qassim Sulaimani Ya Bayar Wajen Dawo Da Alaka Tsakanin Iran Da Saudiya

Abdul Mahdi: Shahid Suleimani ne ya fara kulla yarjejeniya tsakanin Iran da Saudiyya.

Tsohon firaministan kasar Iraki a cikin wani jawabi da ya yi ya bayyana cewa, shahidi Janar Hajj Qassem Suleimani ya aza harsashin yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Iran da Saudiyya na maido da huldar jakadanci.

Rahoton tsohon firaministan Iraqi kan yarjejeniyar da aka yi tsakanin Saudiya da Iran 


Abdul Mahdi: Shahid Suleimani ne ya fara kulla yarjejeniya tsakanin Iran da Saudiyya.


Tsohon firaministan kasar Iraki a cikin wani jawabi da ya yi ya bayyana cewa, shahidi Janar Hajj Qassem Suleimani ya aza harsashin yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Iran da Saudiyya na maido da huldar jakadanci.


Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na yanar gizo na Ahl al-Bait (AS) ABNA ya nakalto maku cewa: Adel Abdul Mahdi cewa, tsohon firaministan kasar Iraki ya gabatar da wani rahota wanda ya sha banban na daban kan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Saudiyya da Iran tare da jaddada matsayin shahidi Qassem Suleimani a cikinta.


Abdul Mahdi ya rubuta a cikin bayanin cewa: Matakin baya-bayan nan da aka yi a birnin Beijing da kuma fitar da sanarwar bangarori uku tsakanin Sin da Saudiyya da Iran na da ma'ana ta tarihi kuma mutane da dama sun taka rawa cikin wannan muhimmin lamari; Lamarin da zai iya sauya fasalin yankin da ma duniya baki daya, batun ba wai batun dawo da huldar da ke tsakanin kasashen biyu ne kadai da ke da sabani ba, har ma da batun yarjejeniyar da aka ce za ta kai ga warware wasu batutuwa masu muhimmanci da kuma na hankali a lokuta masu haɗari.


Ya kara da cewa: "Sabon batu mai matukar muhimmanci shi ne shiga tsakani da kasar Sin ta yi kan wannan yarjejeniya da kuma tasirinta wajen daidaita daidaiton yankin. Zan ambato wasu daga cikin abubuwan da na sani, ko shakka babu wasu sun san wasu abubuwa, yayin da a watan Satumban shekarar 2019 miladiyya Na yi tafiya a hukumance zuwa kasar Sin, kafin ganawar da shugaban kasa da firaministan kasar, shahidi Qassem Suleimani ya kira ni ya ce, "Ko za ka iya zuwa Saudiyya?" saina tambaye shi dalili. Sai yace domin shiga tsakaninmu da kasar saudiya ne batun gaggawa ne. Sai na amsa da cewa, zan tafi Riyadh da zarar na dawo. na fadi wannan bukata ta shahidi Suleimani ga bangaren kasar Sin, kuma sun dauki wannan bukata a matsayin wata alama mai kyau da kuma maraba da ita.


Abdul Mahdi ya ci gaba da cewa: Daga cikin abubuwan da shahidi Shleimani ya bukace su shi ne, za mu taimaka wajen warware rikicin kasar Yemen ta hanyar gwamnatin hadin kan kasa, muna goyon bayan ci gaban dangantakar da ke tsakanin Saudiyya da Iraki da kulla alaka mai zurfi da al'ummar Iraki. "Abu ne mai sauki a tattauna da kasashe makwabta sabanin sauran kasashe, kudurin rage zaman dar-dar na tsawon shekaru 10, mutunta juna bisa daidaiton da ba shi da rinjaye ko kuma aka ci nasara, da tabbatar da zirga-zirga a tekun Fasha, da warware batutuwan da suka shafi Syria da Libya tare. da sauran yankin, da taron ministocin harkokin kasashen waje."


Tsohon firaministan kasar Iraki ya bayyana cewa: "Mun tuntubi 'yan uwa na Saudiyya wadanda suka tambayi dalilin wannan tafiya tare da sanar da su bukatar Iran ta shiga tsakani suka ce shahidi Suleimani ne ya bukaci wannan bukata, sun karbe ta a safiyar ranar 25/9/2019". Mun tashi daga Bagadaza zuwa Saudiyya, sai Mustafa Al-Kazemi (Daraktan Hukumar Leken Asiri a lokacin), Thamer Al-Ghadban, Ministan Man Fetur, da Muhammad Al-Hashemi, Daraktan ofishin Firayim Minista, suka raka ni. A wannan tafiya Sarkin Saudiyya ta yi mana maraba, sannan a sa'o'i na karshe mun yi wata ganawa da yarima mai jiran gado na kasar."


Ya ci gaba da cewa: "A wancan lokacin an kai hari da makami mai linzami kan ma'aikatar man fetur ta Aramco kuma ana zargin Iran da kai harin, duk da cewa kasar ta musanta cewa tana da alhakin wannan harin, a ranar 5/9/2019, Mike Pompeo ministan harkokin wajen Amurka ya kira ya ce. cewa an harba makamai masu linzami daga arewacin tekun Farisa ba daga Iraki bane sabanin jita-jitar da akeyi. Yanayin yana da matukar duhu alokacin yarima mai jiran gadon sarautar Saudiyya yana magana a fusace, da ya gama magana sai muka ce kana so ka yi yaki da Iran, sai ya ce a'a, na ce idan ba ka da niyar yaki ko lamarin zai ci gaba da tabarbarewa da kuma yiwuwar fita daga ikon tsaro a kowane lokaci, ko kuma ku zauna tattaunawa, ya ce, mun gwada wannan lamarin sau da yawa amma ba mu yi nasara ba, na bayyana masa maganin labarin yadda aka warware matsalolin da ke tsakanin Rafsanjani sarki Abdullah yace mene ne shawararku, sai nace mu bude taga, ka rubuta ra'ayinka zamu isar da shi ga bangaren Iran, muna da tabbacin hakan zai kai ga bude tattaunawa, Bin Salman yana da takardar da ke dauke da abubuwa 9 da suka shafi mutunta dokokin kasa da kasa, da zurfin bin hakan, wadanda suka hada da ka'idar kyakkyawar makwabtaka, yakar ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi da raya dangantaka da kasashe makwabta, musamman kasashen yankin da dai sauransu, sannan ya mika su ga hannunsu mu.


Abdul Mahdi ya fayyace cewa: “Mun mika wa shahidi Suleimani wannan takarda da wasu ‘yan sauye-sauye tare da kawata wasu kalmomi tare da cewa: Ka yi aiki mai kyau,yace: zan gabatar da wannan takarda ga shugabannin kasarmu, makonni kadan kafin a kashe shi na tambayi amsar mahukuntan Iran, su ma mahukuntan Saudiyya suna neman amsa, Shahid Suleimani ya ce: "Shugabannin Iran sun binciki wannan al'amari kuma zan ba da amsar da zarar na koma Bagadaza."


Tsohon firaministan kasar Iraki ya ce: "Abin takaici, tsohuwar gwamnatin Amurka ta kai wani harin kisa na matsorata da wauta, kuma ba a samu jaka da amsar Iran da ke tare da shahidi Suleimani ba, na bar mukamin firaminista a ranar 5/7. 2020 kuma al-Kazemi ya zama shugaban gwamnati, kuma a ziyarar aikin da ya kai kasar Saudiyya, an yanke shawarar ci gaba da wannan shiri, kuma an gudanar da tarurruka na farko a karkashin jagorancinsa a Bagadaza da kuma lokacin da ba ya nan a karkashin jagorancin Muhammad Al- Hashemi, shugaban tawagar Saudiyya Khalid Al Hamidan, kuma mataimakin sakatare na bangaren Iran Saeed Irwani, wanda shi ne kwamitin koli na tsaron kasa, kuma an ci gaba da gudanar da tarukan har zuwa lokacin da aka cimma matsaya mai muhimmanci a nan birnin Beijing.


Daga karshe ya ce: Bangarorin biyu sun ci gaba da yin tattaunawar Kuzari, kuma idan ba don ci gaban shiyya-shiyya da na kasa da kasa da karuwar rawar da kasar Sin take takawa ba, da ba a cimma wannan yarjejeniya ba, bangarorin biyu sun ba da tabbacin hakan.