Kafofin yada labaran Isra'ila sun ce an kori 'yan tawagar wannan gwamnati da ta je Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha domin halartar taron kungiyar Tarayyar Afirka a matsayin 'yan kallo, daga zauren taron karkashin jagorancin jami'an tsaro.
Jaridar "Haaretz" ta bayyana korar 'yan Isra'ila daga wannan taro a matsayin wani abu da ba a saba gani ba a taron kasa da kasa.
Mambobin tawagar yahudawan sahyoniya sun shaidawa Haaretz cewa kasashen Afirka ta Kudu da Aljeriya ne ya sa aka kore su daga wannan taro.