Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

19 Faburairu 2023

10:36:40
1347347

Indiya: Wasu mabiya addinin Hindu masu tsatsauran ra'ayi sun kona wasu musulmi guda biyu da ransu

Yan sandan Indiya sun tabbatar da hakan a ranar Asabar din da ta gabata cewa sun kama wani dan Hindu bayan ya kashe wasu musulmi biyu.

'Yan sandan Indiya sun tabbatar da hakan a ranar Asabar din da ta gabata cewa sun kama wani dan Hindu bayan ya kashe wasu musulmi biyu.

  An gano gawarwakin mutanen biyu da aka kona da safiyar Alhamis a cikin wata mota da ta kone a jihar Haryana da ke arewacin kasar, kwana guda bayan sun bace.

Babban Ministan Rajasthan Ashok Jilu ya yi Allah wadai da wannan aika-aika tare da ba da tabbacin daukar tsauraran matakai kan wadanda suka aikata laifin.


Iyalan mutanen biyu wadanda suka fito daga jihar Rajasthan da ke arewa maso yammacin kasar ne suka shigar da kara tare da bayyana sunayen wasu mutane biyar na kungiyar Bajrang Dal ta Hindu mai kishin kasa da tsattsauran ra'ayi a matsayin wadanda suka aikata wannan mummunan aika aika