Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Lahadi

19 Faburairu 2023

10:31:14
1347344

Isra'ila: Zanga-zangar dubban Isra'ilawa tayin adawa da gwamnatin Netanyahu

kimanin Isra’ila 250,000 ne suka sake fitowa kan tituna a fadin kasar domin nuna adawa da shirin yin garambawul ga tsarin shari’a na gwamnatin Benjamin Netanyahu.

kimanin Isra’ila 250,000 ne suka sake fitowa kan tituna a fadin kasar domin nuna adawa da shirin yin garambawul ga tsarin shari’a na gwamnatin Benjamin Netanyahu.

An shafe mako na bakwai ana gudanar da wannan zanga-zangar a wurare sama da 60 a yankunan da aka mamaye. Wannan jarida ta kara da cewa kimanin mutane 135,000 ne suka halarci zanga-zangar a titunan birnin Tel Aviv kadai.

'Yan sandan sun kuma rufe wasu filaye da manyan tituna a daidai lokacin da ake gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Netanyahu, yayin da masu zanga-zangar suka bukaci Netanyahu da ya yi murabus saboda ana tuhumarsa da laifukan cin hanci da rashawa.