Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

11 Faburairu 2023

13:43:11
1345450

Gagarumar muzaharar cika shekaru 44 da juyin juya halin Musulunci a kasar Iran ke gudana a babban masallacin kasa dake Abuja birnin tarayyar Nageriya.

Cincirindon almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) maza da mata ne suka fito muzaharar dauke da tutocin kasar Iran jim kadan da idar da sallan Juma’a a masallacin, tare da gabatar da wakokin taya Iran murna kamar haka. Labbaika Imam Khomaini, Death to America, Death to Israel. Masu muzaharar sun ci gaba da kira ga azzalumar gwamnatin Buhari ta APC kan ta saki passport din Shaikh Zakzaky damai dakinsa Malama Zeenah, ga wasu daga cikin hotunan muzaharar kai tsaye daga Central Mosque Abuja.