Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Asabar

11 Faburairu 2023

10:05:41
1345412

Iran: Anata gudanar da jerin gwano masu tarin yawa na al'ummar Iran a daidai lokacin da ake gudanar da bukukuwan cika shekaru 44 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci karkashin jagorancin Imam Khumaini (Rh).

A yau ne ‘ya’yan al’ummar Iran suka fito muzahara a ranar 22 ga watan Bahman (11 ga watan Fabrairu) domin tabbatar da tsayin dakansu tsatso bayan Tsatso bisa ga madaukakar manufofin da juyin juya halin Musulunci mai albarka, wacce ta ciri tutar tare ​​da sanya fata ga zukatan dukkanin wadanda ake zalunta da kuma suke da rauni a duniya.

A yau ne ‘ya’yan al’ummar Iran suka fito muzahara a ranar 22 ga watan Bahman (11 ga watan Fabrairu) domin tabbatar da tsayin dakansu tsatso bayan Tsatso bisa ga madaukakar manufofin da juyin juya halin Musulunci mai albarka, wacce ta ciri tutar tare ​​da sanya fata ga zukatan dukkanin wadanda ake zalunta da kuma suke da rauni a duniya.


Kamfanin dillancin labaran Ahlal Bayt As ABNA ya habarto maku cewa, an fara gudanar da tattakin tunawa da cika shekaru 44 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a garuruwa 1,400 da gundumomi 38,000 na kasar Iran domin gudanar da bukukuwa mafi girma na juyin juya hali na karni na 20.


A yau ne ‘ya’yan al’ummar Iran suka fito muzahara a ranar 22 ga watan Bahman (11 ga watan Fabrairu) domin tabbatar da tsayin daka daga tsatso zuwa tsatso, bisa ga madaukakar manufofin da juyin juya halin Musulunci mai albarka wanda ya ciri tutarsa ​​da kuma sanya fata ga zukatan dukkanin wadanda aka zalunta da kuma suke da rauni a duniya.


Titunan Tehran babban birnin kasar Iran a yanzu sun cika makil da dubban dubban al'ummar kasar wadanda suka fito kan tituna da wuraren taruwar jama'a domin bayyana goyon bayansu da amincewarsu ga tafarkin shahidan juyin juya halin Musulunci da kuma tafarkinsa mai girma Imam Khumaini. (Allah Ya yarda da shi).


A yau ne shugaban kasar Iran Ayatullah Sayyid Ebrahim Raisi zai gabatar da jawabi a gaban taron jama'a a birnin Tehran, kuma ana sa ran cewa jawabin nasa zai kunshi muhimman matakai (kamar yadda aka sanar).

Bukukuwan bukukuwa da tattaki na bana suna da dadin dandano na musamman, musamman bayan gazawar babban makirce-makircen da aka kaddamar kan Iran din a cikin watannin da suka gabata, inda suka nufi tsaron cikin gida da hadin kan cikin gida a Iran ta hanyar haifar da tarzoma da goyon bayansu ta hanyar siyasa, kafofin yada labarai na yammacin Turai, yakin tattalin arziki da tunani wanda hanyoyinsa mabambanta, amma abin ya faskara kuma ya karye a kan dutse, fadakarwa, taka tsantsan, tsayin daka da hadin kan al'ummar Iran da hikimar jagoranci mai hikima na Shugabannin Iran.

Kamar yadda irin wadannan taruka suke gudana a kasashen masu marawa Iran baya kamar su Najeriya da suma jiya suka gudanar da nasu taurakan taya kasar Iran wannan murna din