Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : IQNA
Laraba

11 Janairu 2023

18:45:02
1337921

Taron jana’izar dan Abdul Basit tare da halartar manya manyan malamai na kasar Masar

An gudanar da jana'izar "Khaled Abdul Basit Abdul Samad" dan Ustad Abdul Basit Abdul Samad, a gaban manya manyan malamai na kasar Masar, ciki har da "Ahmad Ahmed Naina" a masallacin "Hamdiya Shazliyeh" na kasar.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na ABNA ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Yum Al-Seveni cewa, an gudanar da wannanjanaza  ne tare da karatun kur’ani daga manyan makaratun kasar Masar, kuma al’ummar wannan kasa da masu fayyuka a fagen kur’ani su ma sun halarci bikin.

A kwanakin baya ne Khaled Abdul Basit ya sha fama da ciwon suga da safiyar ranar Litinin 9 ga watan Janairu wannan cuta da radadin ya tsananta inda a karshe ya shiga suma kuma ya rasu sakamakon wannan ciwo.

Gidan radiyon kur'ani mai tsarki na kasar Masar da kungiyar mahardata kur'ani da masu karatu na wannan kasa sun fitar da sakonni daban-daban tare da mika ta'aziyyarsu ga iyalai da 'yan uwan ​​Khaled Abdul Basit, musamman Sheikh Tariq Abdul Basit Abdul Samad da Yasir Abdul Basit Abdul Samad. 'yan uwansa biyu.


342/