Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Alhamis

27 Oktoba 2022

20:18:06
1317877

Ana Ci Gaba Da Kira Kan Hukunta Wadanda Suka Aiwatar Da Harin Ta'addanci A Haramin ShahChirag Dake Shiraz Iran

Shugaban Hukumar Shari'ar Iran Ya Bayar Da Umarnin Zakulo Wadanda Suka Kai harin Ta'addanci A Shahcheragh.

Shugaban hukumar shari'a ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa kamata ya yi hukumomin leken asiri, tsaro da jami'an tsaro su gaggauta bibiyar duk masu aikata wannan laifi da kuma musabbabin aikata wannan laifi tare da mika su ga mahukuntan kasar.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Baiti As -ABNA - aya bayar da rahoton cewa, a daidai lokacin da Hujjatul-Islam al-Islam WalMuslimin Muhseni Ajei, shugaban hukumar shari'a ta Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya samu labarin harin ta'addancin da aka kai a haramin Sayyid Ahmad bin Musa (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ina wasu maziyartan suka yi shahada da jikkatar wasu da dama, a lokacin da suka kai ziyara ga shugaban alkalan lardin Fars, yayin da yake jajantawa, ya umurci a yi amfani da dukkanin jami’an tsaro da na ‘yan sanda wajen zakulo wadanda suka aikata wannan aika-aika da shugabannin wannan al'amari mai daci da nadama, da gaggauta shigar da kara a shari'a, da kuma hukunta masu laifi da hukunci mai tsanani.

A cikin sakon ta’aziyyar, shugaban sashen shari’a ya kuma bayyana alhininsa da bakin ciki kan shahadar gungun maziyartan da wasu ‘yan ta’adda ‘yan amshin shata suka shahadantar da su a Harami Ahmad bin Musa (a.s) da ke Birnin Shiraz.

A wani bangare na wannan sakon an bayyana cewa, kiyayya da gaba da makiya al'ummar juyin juya hali da masu hangen nesa na Iran ta kasance ne ta hanyar tabbatar da makirce-makircen da suke da shi na tinkarar matsalar tsaron kasar, a wannan karon sun tunkari maziyartan hubbaren Ahmad bin Musa (a.s) inda su kai ruwan wuta akan su baji ba gani.

A cikin sakon ta’aziyyar shugaban sashin shari’a, ya kara da cewa jami’an leken asiri, tsaro da jami’an tsaro su gaggauta bin diddigin duk masu aikata wannan laifi da musabbabin aikata wannan aika-aika tare da mika su ga hukumomin shari’a na kasa.

A cikin sakon ta'aziyyar Hujjatul-Islam al-Islam wa Muslimin Muhseni Ajei, ya kara da cewa: Ina fatan samun lafiya da jin sauki ga wadanda suka samu raunuka a wannan ta'addanci, ina mika ta'aziyyata da jajantawa iyalan shahidan, da kuma neman hakurin nutsuwar Allah da amincinsa da yardarsa ga shahidan.