Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

20 Satumba 2022

17:19:09
1306761

​Alhuthi: Babban Burin Amurka A Yamen Shi Ne Haifar Da Tashe-Tashen Hankula A Kasar

Jagoran Kungiyar Ansarullah da aka fi sani da Alhuthi a kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Badruddin Alhuthi ya bayyana cewa, babbar manufar amurka a kasar Yemen ita ce mamaye kasar, ko kuma haifar da tashe-tashen hankula a tsakanin al’ummominta.

Alhuthi ya bayyana hakan ne a yau a cikin wani jawabi wanda ya gabatar da aka watsa kai tsaye a kafofin yada labaran kasar Yemen.

Ya ce tun kafin wannan lokacin Amurka ta yi ta hankoron ganin ta haifar da matsaloli a Yemen, wanda hakan zai bata damar mamaye kasar cikin sauki, amma hakan bata samu, sakamakon tsayin daka al’ummar kasar suka yi.

Ya ci gaba da cewa, gazawar Amurka ce ta sanya ta yin amfani da karnukan farautarta na yankin, domin su aiwatar da manufofinta na ruguza kasar Yemen.

342/