Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

20 Satumba 2022

17:18:04
1306759

Quds: Zanga zangar Adawa Da Shirin Isra’ila Na Gurbata Litattafan Karatu

Malamai da daliban makaranta a birnin Qudus sun gudanar da zanga-zangar gama gari ta duna adawa da shirin Isra’ila na gurbata litattafin darrusan karatu a fadin yankunan falasdinawa da ta mamaye.

Dukkan makarantu a fadin yankunan falasdinu da isra’ila ta mamaye sun kasance a rufe tun ajiya litinin domin nuna rashin amincewa da shirin da isra’ila ke yin a gurbata litattafan karatunsu ,da kuma bukatar gwamnatin sahyuniya ta dakatar da yin katsalandam cikin harkokin karatu da dalibai falasdinawa

A farkon wannan watan ne mahukumtan isra’ila suka buga sabbin litattafan karatu da suke kunshe da wasu bayanai na gurbata tarihi da ala’adu da alamomin Falasdinawa

Haka zalika isra’ila ta soke lasisin koyarwa na wasu makarantu a gabashin birnin Qudus da zargin koyar da litattafai masu tayar da hankali kan gwamnatin mamaya. Anasa bangaren ministan Ilimi na gwamnatin Falasdinu Marwan Awartani dake halartar taron koli na babban zauren majalisar dinkin duniya a birnin Newyork yayi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da masu fadaaji das u kare hakkin neman ilimi ga dalibai falasdinawa.

342/