Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

20 Satumba 2022

17:16:42
1306755

​Shugaban Iran Ya Ce Takunkuman Tattalin Arzi, Da Mulkin Kama Karya Su Ne Matsalolin Duniya A Yau

Shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi wanda ya isa birnin New York na kasar Amurka don halattar babban taron MDD karo na 77 ya ce mafi yawan matsalolin da suke addabar kasashen duniya sun taso ne daga mamaya da babakerin kasa guda a kan al-amura.

Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana fadar haka ne jim kadan bayan asowarsa birnin NewYork, shugaban ya ce zai yi amfani da damar da aka bashi na jawabi a babban zauren MDD don bayyana matsayin JMI a cikin al-amura da suke faruwa a duniya.

Ra’isi yace yakamata MDD ta kasance kungiya ce ta kasashen duniya gaba daya, yakamata a ce ta zama kungiya wacce takehakadan kasashen duniya don warware matsalolin da duniya take fama da su.

342/