Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

7 Satumba 2022

16:01:30
1304455

​Abul Gaid: Iraqi Ta Tsallake Hatsarin Fitina Da Ta Tunkareta

Kungiyar kasashen larabawa ta yada da yadda ‘yan siyasa a kasar Iraki suka iya tsallake fitina da ta tunkari kasar a cikin makonnin da suka gabata bayan da magoya bayan gamayyar jam’iyyun Sadar suka mamaye yankin Green Zone na birnin Bagdaza.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Ahmed Abulgaid babban sakataren kungiyar kasahen larabawa yana fadar haka a birnin Alkahira inda cibiyar kungiyar take.

Babban sakataren ya kara da cewa mutanen kasar Iraki sun sha wahalhalu da dama, kowa yana son ganin kasar ta sami nutsuwa a bangaren siyasa tattalin arziki da kuma tsaron kasar.

A cikin watan Octoban shekarar da ta gabata ce aka gudanar da zaben majalisar dokokin kasar Iraki amma har yanzun an kasa kafa gwamnati a kasar saboda sabanin siyasa a tsakanin yan siyasar kasar.

342/