Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

7 Satumba 2022

15:59:28
1304451

Rasha Ta Zargi Amurka Da Hannu Wajen Haifar Da Matsalar Samar Da Gas Ga Kasashen Turai

Kakkain ma’aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bayyana cewa kasar Amurka ce kanwa uwar gami wajen haifar da matsalar dakatar da tura Iskar Gas zuwa kasashen turai bayan da ta ingiza shuwagabanin kasahen daukar matakin yanke huldar tattalin arziki da makamashi tsakaninta da kasar Rasha

Kamfanin dillancin labaran Raueters ya nakalto cewa Kasashen turai na fuskantat mummunar matsalar samar da iskar gas da ba’a taba ganin irinsa ba, inda farashin makamashi yayi tahin goron zabi ,inda masu shigo da iskar gasa a kasar jamus suka fara Tattauna kan batun yi yuwar rarraba iskar gas din bayan da kasar rasha ta rage yawan iskar gas zuwa yammacin turai

Da aka tambaye ta game da lokacin da za’a ci gaba da samar da iskar gas ta bututun Nord Stream 10 kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta rasha maria Zakhariva ta fadi cewa kana yi min tambayar da koda yara kanana ma sun san amsarta domin wadanda suka fara wannan batun su zaku kammala shi,

Ita dai kasar Amurka da kasashen turai suna zargin rasha da daukar matakin nuna son kai kan makamshi bayan da ta rage yawan gas da take fitarwa zuwa ga kwastomominta na kasashen turai , sai dai kasar Rasha ta ce ta fuskanci matsala ne da Naurorinta wanda takunkumin da aka kakaba mata ya hanata gyarawa.

342/