Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

6 Satumba 2022

19:45:15
1304149

​Iran: JCPOA Bata Amincewa Kamfanonin Amurka Shiga Kasar Iran Ba

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa yarjeniyar JCPOA bata amincewa kamfanonin Amurka shiga da kuma gudanar da ayyuka a kasar Iran ba. Ya kuma kara da cewa ko da an farfado da yarjeniyar JCPOA, kamfanonin Amurka ba za su shiga kasar Iran ba.

Kamfanin dillancin labarai IP na kasar Iran ya nakalti Nasir Kan’ani kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya na amsa tambayar da Jaridar Los Angeles Times ta kasar Amurka ta yi, kan cewa idan an farfadoi da JCPOA shin kamfanonin Amurka suna da damar shiga kasar Iran ne?. Sai ya amsa da cewa JCPOA bata amincewa kamfanonin Amurka shiga kasar Iran ba.

Kan’ani ya kara da cewa yarjeniyar JCPOA ta warware wata matsala ce guda kacal, tsakanin Iran da Amurka wacce kuma ita ce, shirint Iran na makamashin nukliya amma bata sauya yanayin dangantaka tsakanin kasashen biyu ba.

Tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran a shekara ta 1979 ne aka katse dangantakar diblomasiyya tsakanin kasashen biyu. Wato foye da shekaru 40 a halin yanzu kenan.

342/