Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

6 Satumba 2022

19:44:19
1304147

​Falasdinu: Sojojin Sahyoniya Sun Kashe Bafalasdine Guda A Jenin A Yau Talata

Wani bafalasdine ya yi shahada a yayinda wasu da dama suka ji rauni a sumamen da sojojin yahudawan sahoyiniyya suka kai da jijjifin yau Talata a birnin Jenin da ke yankin yamma da kogin Jordan wanda HKI take mamaye da shi.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancion labaran WAFA na gwamnatin Falasdinawa yana fadar haka, ya kuma kara da cewa abin ya faru ne bayan da tawagogin sojojin yahudawan tare da rakiyar motocin yaki da buldozoji kimani 100, suka farwa garin sun kuma rufe kofar shiga da fita daga garin a safiyar yau Talata.

Shugaban babbar asbitin Jenin ya bayyana cewa musayar wuta tsakanin bangarorin biyu ne ya yi sanadiyyar shahadar Muhammad Musa dan shekara 29 a duniya da kuma raunata wasu da dama.

342/