Baqiri ya kara da cewa kasahen yankin gabas ta tsakiya sune ya kamata su samar da tsaro a yankin, don haka babu bukatar sojojin wata kasar a cikin ruwan kasa da kasa, yace Ayyukan da sojojin Isra’ila ke aiwatarwa a yankin shi ne ummul habaisin duk wani rashin tsaro da ake fuskanta, kuma ya gargardi kasashen yankin game da wani sakaci na bada dama ga Isra’ila ta sanya kafarta a yankin
Ana sa bangaren kwamandan dakarun sojojin ruwa na kasar Iran Real Admiral Alir riza Tangsiri a watan jiya yayi gargadi game da duk wani hadin guiwa da gwamnatin Isra’ila na haifar da wata barazana da rashin tsaro a yankin tekun fasaha.
Wanna yana zuwa ne adaidai lokacin da dakarun sojin ruwa na kasar iran suka kaddamar da wani jirgin ruwa na yaki da aka kera a cikin gida da aka bashi suna da shahid Qasim Sulaimani babban kwamandan yaki da ta ‘adancin na kasa iran .
342/