Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

6 Satumba 2022

19:41:52
1304144

Iran Tayi Tir Da Harin Da Aka Kai A Ofishin Jakadancin Kasar Rasha A Kabul

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasser Kanaani ya bayyana cewa Iran a yi Tir da harin bomb da aka kai a ofishin jakadancin kasar Rasha da ke birnin Kabul na kasar Afghnistan.

Har ila yau ya kara da cewa kakakin ya bayyana juyayinsa ga gwamnatin kasar rasha da kuma iyalan wadanda harin ya shafa yan kasar Afghanistan da aka kaiwa harin na taa’danci , kana ya bukaci mahukumtan kasar ta Afghanistan da su dauki tsauraran matakai na tabbatar da tsaro a ofisoshin Jakadancin kasashen duniya da wuraren na Diplomasiya a kasar,

Agefe guda kuma kungiyar ta’adda ta ISIS ta sanar da alhakin kai harin a ofishin jakadanci Rasha dake binrin Kabul, da yayi sanadiyar mutane wasu ma’aikatan diplomasiya guda 2, majiyar Asibiti a birnin Kabul ta tabbatar da mutuwar mutane 10 tare da jikkata wasu guda 8 da ke kwance a Asibiti sun samun kulawa.

Ana sasa bangaren ministan harkokin waje na riko na kasar Afghanistan Amir Khan Muttaqi da yake Magana da takwaransa na kasar Rasha Lavrov ya nuna alhinisa game da harin ta’adanci da aka kai a ofishin jakadancin rasha kuma ya sha Alwashin cewa jami’an tsaro kasar za su bada kulawa ta musamman ga ofishin jakadanci na Rasha.


342/