Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Nasir Kan’ani kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran yana fadar haka a safiyar yau a taro da kafafen yada labarai da ya saba gabatarwa a ko wace ranar litinin.
Kan’ani ya kara da cewa manufar kasar Iran a farfado da yarjeniyar JCPOA ita ce ganin an Amurka ta soke dukkan takunkuman tattalin arzikin da ta dorawa kasar da kuma mutanen kasar, tare da wasu sharudda, wadanda da su ne Iran zata amfana da yarjejeniyar.
Yace an gabatar da shawarori da dama kuma daga dukkan bangarorin biyu, amma a halin yanzu Iran ta gabatar da ra’ayinta dangane da shawarorin da kasashen Turai suka gabatar, a halin yanzu muna jiran gwamnatin Amurka ta gabatar da ra’ayinta na karshe.
342/