Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

5 Satumba 2022

17:03:47
1303767

​Yuro Ya Fadi ƙasa Da $ 0.99 A Matakin Mafi ƙanƙanta A Cikin Shekaru 20

Farashin kudin Yuro ya fadi kasa da dala 0.99, matakin da ya kasance mafi karanci cikin shekaru ashirin, bisa la'akari da rashin tabbas da ke tattare da makomar tattalin arzikin Turai, bayan sanarwar da kamfanin Gazprom na kasar Rasha ya fitar a ranar Juma'a kan dakatar da samar da iskar gas ta hanyar bututun Nord Stream zuwa nahiyar turai.

Yuro ya fadi da kashi 0.70% zuwa dala 0.9884 a ranar yau Litinin, wanda shi ne faduwa mafi girma tun daga Disamba 2002, kuma tun daga farkon shekarar nan ne Yuro yake ci gaba da samun koma baya.

Kamfanin na Gazprom ya sanar a ranar Juma’a cewa, za a dakatar da tunkuda iskar gas ta hanyar Nord Stream, domin gudanar da wasu ayyukan gyare-gyare, kuma aikin zai ci gaba har sai an kammala aikin gyaran injinan da ke cikin babban bututun da ke wadata kasashen Turai da iskar gas.

Yanzu haka dai farashin isakar gas da wutar lantarki sun matsanaciyar tsada a kasashen nahiyar turai sakamakon matakain da kasar Rasha ta dauka, wanda hakan yasa wasu kamfanoni suka tsaya cak, yayin da kuma sauran bangarori suke cikin fargaba.

342/