Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

5 Satumba 2022

17:01:45
1303763

Rashin Tsaro Da Zaman Lafiya A Kasar Yamen Na Shafar Yankin Yammacin Asiya Da Tekun Fasha Kai Tsaye

Ministan harkokin wajen kasar iran Amir Abdallian ya fadi hakan ne a lokacin ganawars da manzon musamman na majalisar Dinkin duniya da ya kawo ziyara a birnin Tehran , yana mai bayana cewa rashin tsaro da zaman lafiya daya yakin kasar Yamen ya jawo kai tsaye yana shafar tsaro da zaman lafiyan dukkan yankin yammacin Asiya da kuma tekun fasha,

Har ila yau ministan wajen na iran ya fadi cewa Alummar kasar yamen su ke da hakkin tantance makomarsu da kansu ba wasu daga waje ba, domin lamari ne da babu wand ake jayayya akai game da makomar mutane sama da miliyan 20 a yamen da suka hada da mata yada da suke cikin mawuyacin rayuwa , da suka bukatar magunguna ruwan sha abinci .

Haka zalika ya bukaci jakadan majalisar dinkin duniya kan kasar Yamen da su dauki matakin day a dace wajen dawo da zaman lafiya da tsaro a kasar, sai dai yayi suka game da zagon kasa da kasar saudiya ta kaye a yarjejeniyar datar da bude wuta da aka cimma , kuma ya Jadda muhimmacin dakatar da killacewar da aka yi wa kasar da yaki ya daidaita.

Daga karshe jakadan na Majalisar dinkin duniya Grundberg ya jaddada cewa wajibi ne dukkan bangarorin biyu su dauki mataken da za su taimaka wajen ganin yarjejeniyar tsagaita bude wuta din da aka cimma ta dore,

342/