Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

5 Satumba 2022

17:00:01
1303759

Iran A Shirye Take Ta Sake Gudanar Da Taron Kwamitin Hadin Gwiwa Kan Tattalin Arziki Da Indiya

A wata tattaunawa ta wayar tarho da ta wakana da takwaransa na kasar Indiya ministan harkokin wajen kasar Iran Amir Abdollahian Jaddada shirin Iran na gudanar da sabon taro na kwamatin hadin guiwa na yin aiki tare kan tattalin arziki tsakanin kasashen biyu

Ministocin kasashen biyu sun tattauna dukkan bangarorin biyu sun Jaddada muhimmancin yin aiki tare da kuma fadada dangantakar dake tsakaninsu ta fuskoki daban daban da suka shafi cikin yanki daman a kasa da kasa,

Amir Abdolahiyan ministan harkokin Iran ya fadi cewa ya gamsu da nasarorin da aka samu a ziyarar baya bayan nan day a kai kasar Indiya , yace iran a shriye take ta aiwatar da dukkan yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka rattaba hannu a kai .

Ana sa banagren ministan harkokin wajen kasar Indiya Subrahmanyam Jaishankar shi ya nuna gamsuwarsa game da da matsayin dangantakar dake tsakanin iran da indiya, kana ya nuna fatansa na ganin danagantar dake tsakaninsu ta kara ingnata fiye da kowanne lokaci.

Daga karshe jami’in ya jaddada cewa New Delhi a koda yaushe tana goyon bayan matsayin Iran kan shirinta na Nukiliyya kuma ya tabbatarwa da Abdallahiyan cewa kasarsa zata ci gaba nuna goyon bayanta kan lamarin a nan gaba.


342/