Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

4 Satumba 2022

20:00:12
1303424

Isra’ila : Wani Hari Kan Motar Fasinja Ya Jikkata Sojoji 6

Rahotanni daga Isra’ila, na cewa an jikkata mutum bakwaia da suka hada da sojoji shida da farar hula guda yayin wani hari da aka kai kan wata motar fasinja a arewacin gabar yammacin kogin Jordan dake karkashin mamayar Isra’ila.

Majiyoyin agaji sun ce an dauki wadanda suka jikkata ta jirgi mai saukar ungulu inda aka garzaya dasu asibiti.

Bayan harin dai an ce sojojin Isra’ila dake rike da iko a yankin sun cafke wasu da ake zargi da kai harin, kamar yadda ministan tsaron kasar Benny Gantz, ya sanar.

Babu wani ko wata kungiya data dauki alhakin kai harin, har zuwa lokacin fasara wadanan labaren.

Ko a ranar 14 ga watan Agusta da ya gabata, wani bafalasdine ya yi harbi kan wata motar bas a tsakiyar birnin Kudus inda ya jikkata mutum takwas.

342/