Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

4 Satumba 2022

19:59:23
1303422

“Yan Najeriya Na Ci Gaba Da Bayyana Ra’ayinsu Kan Kyakkyawar Alakar Kasarsu Da Iran Ta Shekaru 50

A wata hira da kamfanin dillancin labaran na kasar Iran yi da Babaji Umar Misau wani babban jami’in diplomasiya kuma tsohon jakadan Najeriya a kasashen Borkina Faso Kenya da Sumaliya ya nuna fatarsa na ganin Najeriya ta ci gaba da amfana da dangantakar dake tsakanin da jamhuriyar musulunci ta Iran ta tsawon shekaru 50

Da yake bayanin game da yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin iran da Najeriya a ranar Asabar 27 ga watan Agustan da ya gabata kan yadda za’a yi aiki tare a bangaren makamashi inda iran za ta taimakawa Najeria wajen gyara matatun manta da suka dade da lalacewa, yace wannan ci gaban da aka samu ya nuna irin yadda tsohuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu take kara kyautatuwa ta fuskar diblomasiya

Ana sa bangaren ministan tsaro na Najeriya Ganaral Bashir magashi a lokacin ganawarsa da jakadan Iran a Najeriya Mohammad Alibak a hedkwatar tsaron kasa dake Abuja ya fadi cewa yanzu ne najeriya za ta gane babbar kawarta ta gaskiya da za ta taimaka mata wajen a bangarori daban daban wajen kawo karshen kalubalen tsaro da suke fuskanta.

342/