Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Alhamis

1 Satumba 2022

20:26:33
1302540

Sakon Ayatullah Makarem Shirazi Zuwa Ga Zaman Taro Na Bakwai Na Majalisar Ahlul-Baiti (as) Ta Duniya

Ayatullah Makarem Shirazi ya aike da sako ga babban taron majalisar Ahlul-baiti AS ta duniya karo na bakwai.

Kamfanin dillancin labaran Ahlul-Bait (a.s) - ABNA – ya kawo maku rahoton cewa, Ayatollah Nasser Makarem Shirazi ya fitar da wannan sako ga babban taron majalissar Ahlul-baiti ta duniya karo na 7.

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, tsira da aminci su tabbata ga Muhammad da alayensa

Da farko ina mika godiyata ga dukkan wadanda suka shirya wannan taro da malamai da masana da manyan malamai da masu fafutukar Shi'a daga ko'ina cikin duniya da suka halarci wannan taro. Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da Ya ba ku nasarar gudanar da irin wannan gagarumin taro mai matukar muhimmanci. Ina fatan za ku amfana daga ayyuka da albarkar man’awiyya na wannan taro mai haske.

Idan aka yi la’akari da fayyace mahangar malaman Shi’a da ma’abota tunani tsawon karnoni masu yawa wajen fahimtar koyarwar Ahlul-Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) da isar da shi ga al’umma, da tsarewa da kiyayewar imani da akida, da jaddada hadin kai a tsakanin musulmi da kuma tabbatar da hadin kai a tsakanin musulmi da kuma tabbatar da mulki da daukakar Musulunci, ina so in ja hankalin ku ga wasu kadan daga cikin batutuwa dangane da hakan.

Na farko; A duniyar yau, zukata da kunnuwa masu son sanin Musulunci da koyarwar Ahlul Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, na karuwa. Wannan wata babbar dama ce da ya kamata a yi amfani da ita wajen hada zukatan masu kishi da masoya da mafi girman darajar ilmin Ubangiji.

Na biyu; Mummunan shirin makiya da masharhanta shi ne shigar da musulmin duniyar musulmi musamman malamansu cikin sabani da cecekuce da ba su da muhimmanci ko maras muhimmanci. Don haka ya kamata a yi taka tsantsan kada a fada cikin wannan tarko, sai dai abi ta hanyar yin riko da igiyar Ubangiji da riko da ababen da suka dace da kuma cin gajiyar hadin kan Kalma daya, ta hakane za aiya wargaza wadannan tsare-tsare da kuma kullace kullacen makirci. Babu shakka addinan Allah da shugabanninsu suna da tasiri a duniyar yau a tsakanin mabiyansu. Haɗuwa da tunani tare da su, baya ga haifar da soyayya tsakanin bayin Allah, zai sa bambance-bambancen su shuɗe ta hanyar haduwar tunani da tausayawa da soyayya.

Na uku; Yana da matukar muhimmanci a samar da yanayi na soyayya da zumunci a tsakanin malaman Shi'a da malamai masu tabligi, musamman a kasashen da musulmi 'yan tsiraru ne. da zai zamo buri da manufa guda daya wato bayyana koyarwar Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su), ya zamo basu bar wata kafa ta yin gasa ba, da tawaya, da tazara a tsakaninsu. Dukkanmu muna kan turba daya ne; Kabilanci, banbancin tsatso, harsuna, kasashe da duk wani abu da hikimar Ubangiji ta bullo da shi a tsakanin mutane kada su haifar da sabani da tazara. Mu yi tunanin hadin kai mu gayyaci mutane zuwa gare shi.

A cikin wannan al’amari mai tsanani ‘yan Shi’a su yi amfani da dukkan karfinsu tare da yin amfani da kayan aikin da suke da su wajen kawar da makirce-makircen makiya da jajircewa wajen kare sirrin ingantacciyar al’adar Musulunci da Shi’a tare da ci gaba da niyya ta ikhlasi na cika sharuddan «وَالَّذِینَ جَاهَدُوا فِینَا لَنَهدِیَنَّهُم سُبُلَنَا». Domin Shiriyar Allah ta hada da su gaba daya.

Kumaya zamo acikin jumla guda, koyarwar Ahlul-Baiti –Alaihis-salam, ita ce tsagaron madogara da take aboyeta an bayyana ta, wacce kuma hatimi ce mai haske mai sanya tunani, da take kashe kishirwa, da haskaka zukata; inda duk lokacin da kuka gwada bin wannan hanyar, za ku zamo tabbatattu.

Ina kara mika godiyata ga dukkan hada wannan taro da wadanda suka halarci wannan taro, kuma ina rokon Allah ya daukaka Musulunci da mabiya mazhabar ta hakika, da nasara ga kowa da kowa wajen sauke nauyin da ke kansa.

Assalamu Alaikum Warahamatullahi Wabarakatuhu

Qom - Nasser Makarem Shirazi


30 ga August, 2022