Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

1 Satumba 2022

20:18:35
1302538

WHO : Mutum 50,000 Suka Kamu Da Cutar Kyandar Biri A Duniya

Hukumar lafiya ta duniya ta ce sama da mutane 50,000 ne suka kamu da cutar kyandar biri tun bayan bullarta a kasashen turai da Arewacin Amurka.

A sabbin alkalumman data fitar WHO, ta ce, an samu mutane 50,496 da suka harbu da cutar sai kuma wasu 16 da cutar ta kashe ye zuwa ranar 31 ga watan Agusta da ya shude.

Amma da alama a cewar hukumar a Amurka kamar a Turai, yawan kamuwa da cutar yana raguwa.


342/