Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Alhamis

1 Satumba 2022

20:15:50
1302532

Kenya : An Fara Zaman Sauraren Karar Zaben Shugaban Kasa

Kotun koli a Kenya ta fara zaman sauraron karar da dan takarar adawa na kasar ya shigar inda yake kalubalantar sakamakon zaben shugabancin kasar na 9 ga watan Agustan da mukayi ban kwana da shi.

Lauyoyin da ke wakiltar dan takarar shugaban kasar, Raila Odinga sun gabatar da kararsu na neman soke nasarar da mataimakin shugaban kasar William Ruto ya samu a zaben shugaban kasar.

Kwamitin alkalai bakwai ne ke sauraren karar da madugun ‘yan adawa na kasar ya gabatar yana mai kalubalantar sakamakon zaben.

A halin yanzu, ana bincike da sake kirga kuri'u a rumfunan zabe 15 da ake korafi akan sahihancin sakamakon su.

Nan da ranar 5 ga watan Satumban nan da muka shiga ne ake sa ran yanke hukunci.

342/