Kasar Amurka ce ta kawo cikas a harjejeniyar da aka cimma a shekara ta 2015 , bayan da ta fice ba tare da wani dalili ba a shekara ta 2018 tare da sake kakabawa iran takunkumi mafi muni duk da hadin kai da iran ta bayar game da dukkan abubuwan da aka cimma yarjejeniya a kai.
Kungiyar Tarayyar Turai a matsayinta na mai shiga tsakani kai tsaye tsakanin Tehran da Washington ta gabatar da bukatarta na farfado da yarjejeniyar nukiliya inda Iran ta bada amsa akai wanda bangarorin tattaunawa suka bayyana shi a matsayin mai ma’ana sosai.
Kasar Amurka ta kwashe makwanni kafin ta bada Amsa ga bukatar da Iran ta gabatar wanda yanzu haka Iran ke nazari akai.
Daga karshe Abdallahiyan ya fadi cewa Iran da gaske take wajen ganin an kulla yarjejeniyar mai dorewa sai dai za’a iya cimma yarjejeniyar idan Amurka ta yi a da ya dace kuma ta karfafa bakatun da aka gabatar mata.
342/