Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

31 Agusta 2022

18:45:45
1302233

Iran: Tattauna Hanyoyin Warware Rikicin Ukraine Na Cikin Ajandar Ziyarar Abdollahian A Moscow

Ministan harkokin wajen kasar ya bayyana cewa, a yau Laraba zai kama hanya zuwa birnin Moscow na kasar Rasha, domin tattauna hanyoyin warware rikicin kasar Ukraine tare da jami’an gwamnatin kasar ta Rasha.

A rahoton kamfanin dillancin labaran IRNA, Ministan harkokin wajen kasar Hossein Amirabdollahian ya bayyana cewa, Babban makasudin ziyarar tasa a birnin Moscow ita ce kokarin warware rikicin kasar Ukraine bisa bukatar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta gabatar.

Sannan kuma ya kara da cewa, Wasu bangarori na kasashen yammacin duniya suna son Iran ta taka muhimmiyar rawar gani a cikin wannan lamari, bisa ga irin kyakkyawar alakar da ke tsakaninta da kasashen Raha da Ukraine.

Ministan harkokin wajen kasar ta Iran ya kara da cewa, baya ga batun Ukraine, bibiyar alakar da ke tsakanin kasashen Iran da Rasha da kuma batun Afganistan ma na cikin ajandar abubuwan da ziyarar za ta kunsa.

342/