Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

31 Agusta 2022

18:45:03
1302231

​Tsohon Shugaban Tarayyar Soviet Mikhail Gorbachev Ya Rasu Yana Da Shekaru 91

Mikhail Gorbachev, tsohon shugaban Tarayyar Soviet day a ragea raye ya rasu yana da shekaru 91 a duniya, a birnin Moscow na kasar Rasha.

Babban asibitin da ke kula da lafiyarsa a birnin ya bayar da sanarwar mutuwarsa a daren jiya Talata, wanda ya ce a cikin wata sanarwa cewa "Mikhail Sergeyevich Gorbachev ya mutu da yammacin yau bayan jinya ta tsawon lokaci."

A cewar kamfanin dillancin labarai na TASS, Gorbachev yana kwance a asibitin ne tun bayan bullar cutar Covid-19, bisa bukatar likitocinsa, kuma tun daga lokacin yana karkashin kulawar likitoci.

Za a binne Gorbachev a makabartar Novodevichy da ke Moscow kusa da matarsa Raisa, wacce ta rasu a shekarar 1999, kamar dai yadda kamfanin dillancin labaran TASS ya nakalto daga wata majiya ta iyalan mamacin.

Gorbachev Mutum ne dai da magoya bayansa suke ganin ya taka muhimmiyar rawa wajen kawo karshen yakin cacar baka tsakanin Tarayyar Soviet da kasashen yammacin turai, yayin da masu adawa da shi ke zarginsa da taimakawa wajen faduwar Tarayyar Soviet.


342/