Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

29 Agusta 2022

17:37:10
1301667

Ministan Harkokin Wajen Iraki Yana Ziyarar Aiki A Birnin Tehran

Kakakin Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iraki Ahmad Al-sahaf ya bayyana cewa minsitan harkokin wajen kasar Fua’ad hussaini zai kawo ziyarar aiki a nan birnin Tehran inda zai gana da manyan mukarraban gwamnatin kasar,

Shiga tsakanin da kasar Iraki ke yi a tattaunawar da ake na kyautata dangantaka tsakanin kasashen Iran da kasar Saudiya na daga cikin muhimman baautuwan da zasu mamaye tattaunawar,

Jakadan kasar Iran a Kuwait ya fadi cewa saboda irin ci gaban da aka samu a kasar iraki a baya bayan nan ana shirye-shiryen fara zagaye na 6 na tattaunawa tsakanin Tehran da Riyad , kuma tana jiran kasar Iraki ta bayyana aniyarta na karbar bakunci tattaunawar a Iraki , kwamitocin kasahen iran da Saudiya a shirye suke su koma tebirin tattaunan kan wannan batun.

Haka zalika ya kara da cewa tuni aka amince game da batun komawa teburin tattaunawa tsakanin bangarorin biyu zagaye na 6 sai dai ana jiran a samu wani yanayi da ya fi dacewa dacewa

342/