Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

29 Agusta 2022

17:36:31
1301666

​Kasar Ethiopia Ta Bayyana Aniyarta Ta Tattaunawa Kan Madatsar Ruwar Da Ake Ce-ce- Ku-ce A kai

Jakadan kasar Ethiopia a kasar Sudan Yatal Amiru ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta tattauna da kasashen masar, Sudan game da takaddamar da ake yi kan batun madatsar ruwa da take ginawa a tekun nilu bisa shiga tsakanin kungiyar tarayyar Afrika.

Da yake tattaunawa da manema labarai jakadan na habasha ya fadi cewa game da batun madasatar ruwa cewa an kammala gina ta cikin nasara, kuma bai cutar da Masar ko Sudan ba, kuma babu wani tasiri da yayi ga kasashen biyu game da ruwan da suke samu

Wasu bayanai sun nuna cewa a ranar 11 ga watan Agustan da muke ciki ne gwamnatin habasha ta sanar da fara aiki da inji na biyu wajen samar da karfin wutar lantarki, kuma haka yana zuwa ne adaidai lokacin da ake zaman tankiya tsakanin Adis Ababa da bangaren Sudan Masar saboda korafin da kasashen biyu suka yi na tasirin da madatsar ruwan za ta yi kan ruwan da suke amfani da shi a tekun nilu

A ana bangaren kasar Masar ta aike da wasika zuwa ga shugaban kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya game da sabon matakin da kasar Habasha ta dauka na fara samar da karfin wutar lantarki a madatsar ruwan da ta gina da hakan zai cutar da kasar sosai.


342/