Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

29 Agusta 2022

17:36:08
1301664

​Raeisi: Iran Ta Samu Gagarumin Ci Gaba A Bangaren Ayyukan Nukiliya

Shugaba Ibrahim Raeisi ya ce yarjejeniyar farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran ta ta'allaka ne kan daidaita batutuwan da suka shafi lamuni da kariya tsakanin Tehran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA.

Raeisi ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai a ranar Litinin din da ta gabata wanda ya samu halartar 'yan jaridun cikin gida da kuma wakilan kafafen yada labarai na kasashen waje a Tehran babban birnin kasar.

Ba tare da warware waɗannan batutuwan ba, sake farfado da yarjejeniyar 2015 da aka sani da Shirin Haɗin gwiwa na Ayyuka (JCPOA) ba shi da ma'ana.

A baya-bayan nan ne hukumar ta IAEA ta bukaci Iran da ta yi bayani kan abubuwan da ta ce ta gano na inganta sinadarin Uranium a wasu wuraren da ba a bayyana ba.

Tehran ta bukaci hukumar da ta yi watsi da zarge-zargen da take yi wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran wanda galibi ke fitowa daga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.

A yayin taron manema labarai a ranar litinin, Raeisi ya kuma yi watsi da barazanar da Isra'ila ke yi wa Tehran, yana mai jaddada cewa babu wanda zai iya tauye wa al'ummar Iran 'yancinsu na samun fasahar nukiliya cikin lumana.

"Mun sha bayyanawa sau da yawa cewa makaman nukiliya ba su da gurbi a cikin rukunanmu na nukiliya. Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya sha bayyana cewa mallakar irin wadannan makamai haramun ne a addinance. Mun kuma bayyana a cikin manufofinmu na ketare cewa wadannan makamai ba su da gurbi a manufofinmu na ketare,” ya kara da cewa.

Raeisi ya kara da cewa Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu babban ci gaba a bangarori daban-daban na masana'antar nukiliya, wato a fannin mai da makamashi, kuma a baya-bayan nan an baje kolin nasarorin da aka samu yayin wani baje koli.

342/