Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

29 Agusta 2022

17:34:36
1301661

Turkiyya Ta Yi Tir Da Kalamman Macron A Aljeriya

Turkiyya ta yi allawadai da wasu kalammai da shugaban kasar faransa Emmanuel Macron, ya furta yayin ziyararsa a kasar Aljeriya, inda ya zargi wasu kasashen duniya ciki har da, Turkiyyar da rura wutar kin jinin faransa a nahiyar Afrika.

Wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Turkiyya ta fitar ta yi tir da zarge-zargen da ta danganta da marar tushe da Macron ya yi, tana mai bukatarsa da ya waiwayi salon mulkin mallakar da faransa ta yi wa wasu kasashen nahiyar wanda ya janyo mata bakin jini a nahiyar.

Sanarwar ta ce "kalaman Shugaba Macron rashin ta fadi ne, duba da irin rawar da Faransar ta taka a yayin mulkin mallakarta a wasu kasashen nahiyar.

Shi dai Shugaba Macron yayin ziyarar tasa a kasar Aljeriya, ya zargi wasu kasashen duniya ciki har da Rasha da China da Turkiyyar da hannu wajen ingiza wutar kin jinin Faransa da wanzuwa tamakar wutar daji a nahiyar ta Afirka.

342/