Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ابنا
Litinin

29 Agusta 2022

06:43:31
1301394

Shugaban Majalisar Ahlul-Bait (AS) Ta Duniya

Sakon Ta'aziyyar Babban Sakataren Majalisar Ahlul-Bait (AS) Ta Duniya Na Rasuwar Ayatullah Naseri

Bayan rasuwar Ayatullah Naseri daya daga cikin malaman Isfahan, babban sakataren majalisar malamai ta Ahlul-Bait (AS) ta Duniya ya fitar da sakon ta'aziyya.

Kamfanin dillancin labaran Ahl al-Bait (AS) -ABNA- ya habarta cewa, bayan rasuwar Ayatullah Naseri daya daga cikin malaman Isfahan, babban sakataren majalisar malamai ta Ahlul-Bait (AS) ta Duniya ya fitar da sakon ta'aziyya.

 

Nassin sakon Ayatullah Riza Ramezani shi ne kamar haka;

 

بسم الله الرّحمن الرّحیم

إِنَّا لِلَّٰهِ وَإِنَّا إِلَيْهِ رَاجِعُونَ

 

 Rasuwar malamin nan masanin ubangiji kuma masanin Aklak da ilimomi marigayi Ayatullah Haj Sheikh Muhammad Ali Naseri (ra) ya haifar da radadi da tasiri sosai.

 

Shi dai wannan malami mai tsoron Allah da yake a lardin Isfahan, ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen ilmantarwa da yada koyarwar kur'ani, da inganta mazhabar Ahlul Baiti (amincin Allah ya tabbata a gare su) da yi wa al'umma hidima da wadanda suke mabukata.

 

Babu shakka rasuwar wannan malami kuma malamin mai koyar da tarbiya, wanda ya janyo hankalulan mutane da yawa tare da karkato zuwa ga addinin Allah da mazhabar Ahlul Baiti, tsira da amincin Allah su tabbata a gare su, ta hanyar anfani da ruhinsa da halayyarsa, rashi ne ga Musulunci da makarantun hauza, wanda shi ke maye guribnsa abu ne mai wahala, da kuma rashin kasancewarsa bisa la'akari da muhimman bukatun da al’ummar suke da shi na samuwarsu acikin zai zama bayyananne ga masana a cikin al'umma.

 

Ina mika ta'aziyyata na wannan musiba mai raɗaɗi ga mai girma jagoran juyin juya halin Musulunci, da manya-manyan maraji’an Taqlid, da makarantun hauza, mutanen Isfahan, ga ya gida mai girma, musamman ma 'ya'yan wannan malami masanin Ubangiji, almajiransa da sauran masu kaunarsa, ina rokon Allah Ta’ala ya girmama daukakar wannan malami da muka rasa kuma yaa tashe shi tare waliyansa tsarkaka, ga kuma iyalansa da sukai saura ya basu haƙuri da lada mai yawa.

 

Reza Ramezani