Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

28 Agusta 2022

18:31:27
1301323

Nijer Zata Yi Amfani Da Sinadarai Don Kara Yawan Ruwan Sama A kasar

Gwamnatin Nijer ta kuduri anniyar kara yawan ruwan sama a kasar ta hanyar amfani da sinadarai, don magance karancin ruwan sama a kasar wanda ya jawo karancin abinci.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya nakalto hukuma mai kula da al-amuran yanayin kasa tana fadar haka. Ta kuma kara da cewa a cikin farkon watan Augustan mai karewa ta yi amfani da wannan fasahar a birnin Yemai babban birnin kasar bayan an sami karancin ruwan sama na makonni biyu.

A cikin wannan aikin dai ana amfani da jiragen sama don baza sinadaran Silver, Soduim da kuma acetone a sararin samaniyar inda ake yin ruwa don samar da hadari mai nauyin da zai yi ruwan sama bayan wani lokaci.

Katiellou Gaptia Lawan, darakta mai kula da hukumar ya fadawa AFP kan cewa suna aiki tare da kamfanin jiragen sama na IBI AIR na kasar Mali don cimma wannan manufar. Banda haka lawal ya kara da cewa zasu fi maida hankali kan yankunan kiwon dabbobi don samar da shiyayin dabbobi.

342/