Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Lahadi

28 Agusta 2022

18:27:36
1301313

Madagaska : Kotu Ta Tabbatar Da Daure ‘Yan Faransa 2 Bisa Yunkurin Juyin Mulki

Wata babbar kotu a Madagaska ta tabbatar da hukuncin dauri ga ‘yan faransa biyu bisa zarginsu da kisa juyin mulki da kuma yunkurin kashe shugaban kasar.

Faransawan biyu dai an yanke musu hukuncin dauri ne na shekara ashiri da kuma aikin dole na shekara goma.

A watan Yuli ne lauyoyin masu zargin suka bukaci soke hukuncin da kotun kula da manyan laifuka ta Madagska ta yanke a watan Disamban 2021.

Saidai bayanai sun ce akwai yiyuwar faransawan su nemi a basu damar gduanar da zama gidan yarin a kasarsu faransa.

342/