Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

26 Agusta 2022

19:58:10
1300885

Iran : Ba Zamu Lamunci Zarge-zarge Marar Tushe Na Hukumar IAEA Ba

Iran, ta bakin ministan harkokin wajen kasar ta ce ba zata lamunci wasu zarge zarge marar tushe da hukumar IAEA, ke yi a daidai lokacin da tattaunawar neman ceto yarjejeniyar nukiliyar 2015, ta zo gabar karshe.

Babban jami’in diflomatsiyan na Iran, Hossein Amir Abdollahian, ya ce, zarge zargen da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ke yi ya nuna yadda hukumar ta zama ‘yar amshin shaten Isra’ila.

Amir Abdollahian, ya ce Iran ta samu amsar Amurka game da shawarwarin karshe data gabatar ta hanyar kungiyar tarayyar turai, kuma ta ce abinda ta fi ba karfi shi ne samun tabbaci daga Amurka game da duk wata yarjejeniya da za’a cimma.

Kalamman na Iran dai na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ta bi sahun masu kamfen din adawa da duk wani yunkuri na cimma yarjejeniya da Iran.

342/