Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

26 Agusta 2022

19:57:24
1300883

​Iran Da Najeriya Sun Jaddada Aniyarsu Ta Karfafa Alaka Ta Fuskar Tsaro

A wata ganawa da ya yi da jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Abuja, Ministan Tsaron Najeriya ya jaddada ci gaba da karfafa alaka ta fuskar ayyukan tsaro a tsakanin Najeriya.

A cewar rahoton "Daily Post", ministan tsaron Najeriya "Bashir Magashi" ya karbi bakoncin jakadan Iran "Mohammed Alibek" a hedikwatar ma'aikatar tsaron kasar da ke "Abuja" a ranar jiya Laraba.

Ministan tsaron Najeriya ya shaidawa jakadan kasar Iran cewa Najeriya , Najeriya na mai da hankali ga kawayenta na gaskiya da neman goyon bayansu, yayin da kasar ke yaki da ayyukan da ke barazana ga zaman lafiyarta.

Magashi ya bukaci Alibek da ya samar da hanyoyin da suka dace don kulla kyakkyawar hulda tsakanin sojojin kasashen biyu.

Idan dai ba a manta ba a kwanakin baya ne kasashen Iran da Najeriya suka rattaba hannu kan wasu takardu na hadin gwiwa guda 9 a fannonin al'adu, yawon bude ido, man fetur, noma, wasanni da kasuwanci.

An gudanar da taro na shida na kwamitocin hadin gwiwa na Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Tarayyar Najeriya a birnin Tehran tare da halartar Seyed Reza Fatemi Amin ministan masana'antu da ma'adinai da ciniki na Iran, da kuma ministan harkokin wajen Najeriya Alh. Zubairu Dada.

342/