Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Jummaʼa

26 Agusta 2022

19:55:54
1300879

Angola : Jam'iyya Mai Mulki Ce Ke Kan Gaba A Zaben Shugaban Kasa

Rahotanni daga Angola na nuni da cewa jam'iyya mai mulkin a kasar ta MPLA ce ke kan gaba a sakamakon zaben shugabancin kasar da ake fitarwa.

Hukumar zaben kasar ta ce cikin kaso 80 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben, jam'iyyar shugaba Joao Lourenço, ce ke kan gaba wadda kuma ta shafe shekaru fiye da 40 tana mulki a kasar.

MPLA na da kaso 53 cikin 100, yayin da jam'iyyar adawa ta Unita ke da 43 cikin 100, na kuri'un da aka kirga a baya bayan nan.

Saidai tun da farko jam'iyyar Unita ta ce bayanai sun nuna cewa ita ke kan gaba.

342/