Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

24 Agusta 2022

19:11:35
1300634

​Angola: A Yau Ne Ake Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa Da Na ‘Yan Majalisa

Gidan Rediyon Faransa ya bayar da rahoton cewa, a yau ne al’ummar Angola ke kada kuri’a a zaben ‘yan majalisar dokoki wanda zai bai wa dan takarar jam’iyrar da ta samu rinjaye damar zama shugaban kasa, wato dai tsakanin shugaba mai ci Joao Lourenco da jagoran adawa Adalberto Costa Junior.

Angola wace duk da kasancewarta kasa ta biyu mafi yawan arizikin man fetur a nahiyar Afrika da ke kudancin sahara, haka kuma ta 3 mai arzikin Lu’ulu’u a nahiyar, har yanzu kasar na ci gaba da kasancewa daya daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya.

A cikin wani hasashe da babban bankin duniya ya yi a 2020 ko wane dan Angola daya a cikin biyu na rayuwa ne da kasa da dalar Amurka 1,90 a wuni guda.

To sai dai idan har shugaban kasar Joao Lourenco da aka zaba a 2017 ya kasance dan takarar da ke neman maye kansa a zaben na yau laraba, za a iya cewa ya dogara da sauye sauyen tattalin ariziki da ya samar wadanda yanzu haka suka dan farfado da tattalin arizikin kasar.

Zaben na yau majalisun dokoki da ‘yan Angola za su gudanar zai bai wa dan takarar jam’iyar da ta samu rinjaye ne damar darewa kujerar shugabancin kasar.

Angola wadda Portugal ta yi wa mulkin mallaka tun ashekarar 1975 jam’iyyar MPLA ke mulkinta sai dai a wannan karon al’amura ka iya sauya la’akari da yadda ake kankankan tsakanin jam’iyyar mai mulki da hadakar bangaren adawa.

Mafi rinjayen al’ummar Angola miliyan 33 na cike da fatan samun sauyin ta fannin tattalin arziki ga kasar da a baya ta sha fama da yakin basasa.

342/