Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

24 Agusta 2022

19:11:12
1300633

​Farashin Danyen Man Fetur Ya Sake Yin Tashin Gwauron Zabi A Kasuwanninsa Na Duniya

Farashin danyen man fetur yana ci gaba da kara hauhawa a kasuwanninsa na duniya, inda mai na "Brent" farashinsa ya haura dalar Amurka 101 a kowace ganga a yau Laraba, wanda shi ne karon farko tun daga ranar 3 ga wannan wata na Agusta.

Da karfe 11:50 na safiyar yau agogon Moscow, danyen mai na Amurka "West Texas Intermediate" ya tashi da kashi 1.28% zuwa $94.94 a kowace ganga daya, yayin da kuma farashin danyen mai na Brent ya tashi da kashi 1.32% zuwa dala 101.4, a cewar kafar yada labarai ta Bloomberg.

Tashin farashin dai ya biyo bayan rahotannin da kafofin yada labarai suka bayar, da ke cewa majiyoyin kungiyar ta OPEC +, wadda kungiyar da ta hada da Rasha da Saudiyya, na iya matsawa wajen rage yawan man da ake hakowa a kowace rana, idan aka samu cikas bayan cimma yarjejeniya tsakanin Iran da kasashen yammacin Turai kan yarjejeniyar nukiliya, da kuma dage takunkumin da aka kakabawa kasar ta Iran.

342/