Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

24 Agusta 2022

19:10:28
1300631

Iran: Babu Kulla Yarjejeniya Tsakaninmu Da Kasashen Turai Sai Hukumar Nukiliya Ta Janye Zargin Da Ta yi Mata

Mai bada shawara ga tawagar kasar iran a tattaunawar cire mata takunkumi a birnin Vieanna na kasar Austiriya ya bayyana cewa babu batun cimma wata yarjejeniya tsakaninta da bangaren kasahen turai matukar hukumar kula da makamshin nukiliya ta duniya ba sai kwamitin gwamnoni suka dakatar da rohon da aka mika masa da kuma zargi mara tushe da take yi wa kasar iran.

Maohammad Marandi yayi wannan bayanin nan a wani sako day a aike da shi a shafinsa na Tweter da yake mayar da martani game da rahoton da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yada dake nuna cewa kasar Iran ta ajiye wasu daga cikin muhimman bukatunsa a tattaunawar da ake yi.

Yace babu batun kulla yarjejeniya matukar hukumar nukiliya ta duniya bat a soke zargin karya da ake yi wa iran ba, da kuma cire dakarun kare juyin musulunci na iran daga cikin jerin sunyen yan ta’adda da amurka ta yi, to babu batun cimma matsaya a vieanna

Wanna yana zuwa ne adaidai lokacin da kasar Amurka ta nuna cewa tana ci gaba da yin nazari kan amsar da iran ta bayar kan bukatar da aka mika mata, kuma ana sa ran za ta bada amsa ayau din nan.

342/