Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Laraba

24 Agusta 2022

19:08:21
1300626

​Iran: Kasashen Waje Na Da Hannu A Yaduwar Ayyukan Ta’addanci A Yammacin Asia da Afirka

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hussain Amir Abdullahiyan ya bayyana cewa wasu kasashen waje na da hannu a samuwar kungiyoyin yan ta’adda a kasashen yammacin Asia da kuma Afirka.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan ya na fadar haka a taron yan jaridu na hadin guiwa da tokwaransa na kasar Mali Abdoulaye Diop a birnin Bamako babban birnin kasar Mali a jiya Talata.

A wani banagare na jawabinsa ministan ya bayyana anniyar kasar Iran ta fadada dangantaka tsakaninta da kasar Mali, musamman a bangarorin tattalin arziki da kuma tsaro.

Abdullahiyan ya ce shawararsa ita ce kasashen da suke fama da matsalolin yan ta'adda su yi fada da ayyukan ta’addanci da kuma kungiyoyin yan ta’adda da kansu, ba tare da sanya hannun kasashen waje cikin lamarin ba. Ana saran ministan zai ziyarci wasu kasashen gabacin Afirka kafin ya kammala ziyararsa a nahiyar.

342/