Mahukumta a kasar sun bayyana cewa yanzu haka ma’aikatan kwana-kwana na ci gaba da gudanar da ayyukan jin kai na gano Gawawwakin wadanda abin ya shafa, da ake ganin akwai yi yuwa adadin wadanda suka mutu ya karu,
A duk lokacin Zafi Arewacin kasar Aljeriya na fuskantar matsalar gobarar daji sai dai wannan bala’in na kara yawa a kowacce shekara saboda canjin yanayi dake haifar da fari da tsananin zafi, masana sun dora alhakin nakasun da aka samu a kan karacin kayan aiki na kashe gobara da wadataccen ruwa da kuma rashin kula da gandun dajin.
342/