Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Talata

23 Agusta 2022

16:47:00
1300324

​Kanaani: Amurka Tana Jan-Kafa Wajen Bayar Da Amsa Kan Shawarwarin Da Iran Ta Gabatar

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasser Kanaani ya bayyana cewa, martanin da muka bayar kan kudirin da kasashen Turai suka gabatar dangane da batun farfado da yarjejeniyar nukiliyar ya dace da lokaci, kuma bai saba wa ko daya daga cikin abubuwan da muka sanya hannua kansu bat un daga farko, amma har yanzu ba mu samu martani daga bangaren Amurka ba.

Kanaani ya bayyana haka ne a taron manema labarai na mako-mako da yake yi a yau Litinin, yayin da yake amsa tambaya kan tattaunawar Vienna, ya ce: Batutuwan da suka rage a tattaunawar ba su da yawa, amma suna da muhimmanci kuma dole ne a amince da su, ba tare da kauce wa sharuddan da muka gindaya ba.

Ya kara da cewa muna son yarjejeniyar da za ta gamsar da al'ummar Iran tare da kiyaye maslaharta, yana mai cewa: Idan Tehran na bukatar yarjejeniya to kasashen Turai da Amurka su ma suna bukatar hakan.

Ya jaddada cewa jinkirin da Amurka ta yi da shirun da Turawa suka yi da kuma matsin lamba na masu tsattsauran ra'ayi da suke da tasiri a kan gwamnatin Amurka da kasashen turai, wannan ya sa har yanzu tattaunawar tana yin tafiyar hawainiya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ya yi nuni da cewa, yahudawan sahyoniyawan suna taka mummunar rawa a cikin wannan tattaunawa, kuma suna yin tasiri a kan gwamnatin Amurka, saboda haka dole ne Washington ta yanke shawara bisa muradunta.

342/