Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

30 Mayu 2022

11:21:00
1262224

​Najeriya: NCDC Ta Tabbatar Da Kamuwar Mutane 21 Da Cutar Kyandar Biri

Hukumomin kiwon lafiya a tarayyar Najeriya sun tabbatar da kamuwar mutane 21 da cutar kyendan biri daga farkon wannan shekara zuwa yansu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Hukumar NDCD mai yaki da cututtuka masu yaduwa ta bayyana cewa daga cikin mutane 61 da suke hasashen suna da alamun cutar, 21 sun kamu da ita, a yayin da daya daga cikinsu dan shekara 40 aduniya ya rasa ransa saboda cutar.

An saba samun cutar kyendan biri a kasashen Kamaru, Afirka ta tsakiya, Democdiyyar Kongo da kuma Najeriya a baya. Amma cutar ta fara jawo hankali a lokacinda mutane kimani 200 sun kamu da ita a kasashen 19 a nahiyar Turai a cikin watan mayun da muke ciki,amma babu wanda ya mutu.

342/