Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Hausatv
Litinin

30 Mayu 2022

11:20:10
1262223

​Iran Da Iraki Suna Neman Hanyoyi Yaki Da Hadarin Kura Da Kuma Sauyin Yanayi

Jami’an gwamnatin kasashen Iran da Iraki suna neman hanyoyin yaki da bala’in hadarin kura da kuma sauyin yanayi a kasashen yankin.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - na kasar Iran ya nakalto mataimakin shugaban kasar Iran Ali Salajeqi da kuma firai ministan kasar Iraki Mustafa Al-kazimi suna fadar haka a gawanar da suka yi a jiya Lahadi a birnin Bagdaza babban birnin kasar Iraki.

Bangarorin biyu sun bukaci dukkan kasashen da abin ya shafa su gaggauta daukar mataki don shawo wannan wannan bala’in na sauyin yani da kuma hadarin kura wanda yake shafar lafiyar mutanen kasashen yankin.

342/